Sanata Barau I Jibrin

Me ka ke nema?


Shafin Farko

Sanata Barau I Jibrin



Sanata Barau I Jibrin
Hoto:www.oak.tv

Gabatarwa

Maliya, damina baki mugunta, mikiya mai hangen nesa, suna daga cikin irin kira-kiraren da Kanawa ke yi wa Sanata Barau I Jibrin.

Mutum ne shi fasihi, mai haƙuri, biyayya, juriya da kuma son kyautatawa jama’ar da yake wakilta.

Akawu (accountant) ne shi, masani a fannin kasuwanci da hada-hadar kuɗaɗe, wanda daga baya ya zama fitaccen, gogaggen ɗansiyasa. Tabbasa karansa ya kai tseko a harkar siyasa domin yana da gogayyar shekaru ashirin da ɗoriya a harkar siyasa. Muna fata wannan rubutu ya fito wa da mai karatu mutunkar wannan bawa Allah.

Haihuwa

An haifi Sanata Barau I Jibrin a shekarar 1959 a garin Kabo wanda yanzu ya zama helikwatar mulkin ƙaramar hukumar Kabo a Jihar Kano da ke Najeriya.

Karatu

Sanata Barau ya yi karatun firamare da sikandire kamar yadda aka saba. Daga baya kuma ya samu nasarar yin karatun digiri a fannin akawu (accounting).

Bayan kammala digirin farko, ya samu horon ƙwarewa a fannin gudanar da kuɗi da kuma yi wa kayayyaki farashi (Masters Certificate in Financial Management and Pricing). Ya sake samun wani horon na ƙwarewa a fannin gudanarwa (Masters Certificate in Management). Sai kuma karatun digiri na biyu a fannin gudanar da kasuwanci (Masters of Business Administration (MBA)). Daga ƙarshe ya sake karɓar wani horon ƙwarewa a fannin gudanar da kuɗaɗe domin yanke hukuncin kasuwanci (Certificate in Financial Management for Business Decisions) daga fitacciyar jami’ar Cornel University da ke Tarayyar Jihohin Amurka (United States of America).

Waɗannan karatuttuka da kwasakwasai, su suka tabbatar da zamowarsa akawu sannan kuma masani a fanni kasuwanci da hada-hadar kuɗaɗe.

Gogayyar Aiki

Bayan kammala karatuttukansa, Sanata Barau I Jibrin ya yi aiki a fannin akawu na Gidauniyar Jahar Kano (Kano State Foundation) na gajeren lokaci, daga baya ya kafa kamfani mai zaman kansa da ke hada-hadar ƙere-ƙere (manufacturing), lamuni (insurance) da kuma gine-gine (construction).

Siyasa

Kunnowar jamhuriya ta biyar a siyasar Najeriya wadda ake cikinta tsindim a yau, Barau ya bayyanar da sha’awarsa ta shiga siyasa domin hidimtawa jama’a. Wanda kuma cikin taimakon Allah ya yi abin nan da ake cewa siri-ɗaya-ƙwale. Takararsa ta farko ya samu ɗarewa kujerar wakilci a Majalisar Wakilai ta Tarayya. Tun daga wancan lokaci ake damawa da shi har zuwa yau, abin da ya bashi damar samun shekaru 22 cur (1999 – 2021) ana damawa wa da shi a siyasar Najeriya.

Muƙaman Siyasa

  1. 1999 – 2003: Ya zama ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Tarauni da ke Jahar Kano.
  2. 2003 – 2007: Shugaban Kamfanin Kadarori da Hannun Jari na Jahar Kano (Kano State Investment and Properties Limited).
  3. 2011 – 2015: Kwamashinan Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha (Ministry of Science and Technology) ta Jihar Kano.
  4. 2015 – 2019: Sanata; ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Kano ta Arewa.
  5. 2019 zuwa ya: Sanata; ɗan majalisar dattawa mai wakiltar Kano ta Arewa a karo na biyu.

Ƙudurori A Majalisar Ƙasa


Sanata Barau I Jibrin Yana Gabatar da Ƙuduri a Zauren Majalisar Dattawa
Hoto:The Guardian

Ƙudurorin da Barau ya miƙa wa Majalisar Ƙasa suna da tarin yawa, wasu daga ciki sun zama dokoki tare kuma da haifar wa ƙasa ɗa mai ido, wasu kuma an yi musu karatun farko, wasu kuma suna kan layi. Amma fitattu kuma waɗanda suka zama taurarri ba wai kawai gare shi ba, a’a, har ma da gwamnatin APC sannan kuma suka zama sanyin zuciya ga jama’ar ƙasa akwai:

  1. 2016: Tare da haɗin guiwar wasu, Sanata Barau ya gabatar da Ƙudurin Haramta cin Zarafin Jinsi a Manyan Marantu (Sexual Harassment in Tertiary Educational Institutions Prohibition Bill, 2016). Wannan ƙuduri ya samu waucewa.
  2. 2019: Ƙudurin Samar da Makarantar Fasahar ta Tarayya a Kabo (Federal Polytechnic Kabo). An yi wa ƙudurin karatun farko.
  3. 2019: Ƙudurin samar da cibiyar kimiyyar ƙwayoyin halittu ta Najeriya (Microbiology Council of Nigeria). An yi wa ƙudurin karatun farko.
  4. 2019: Ƙudurin kafa Hukumar Haɓɓaka Arewa-Maso-Yamma (Norht-West Development Commission). An yi wa ƙudurin karatun farko da na biyu sannan aka miƙa shi hannun kwamatin da ya dace domin su nazarce shi tare da bayar da rahoton ƙarshe.
  5. 2019: Ƙudurin Shirin Cigaba (Project Continuity). Ƙudurin yana hannun kwamatin da ya dace.
  6. 2019: Ƙudurin Samar da Jami’ar Aikin Gona ta Tarayya a Ɗanbatta, Jihar Kano (Federal University of Agriculture Ɗanbatta Kano State). An yi wa ƙudurin karatun farko da na biyu tare da miƙa shi hannun kwamatin da ya dace domin bayar da shawara.
  7. 2019: Ƙudurin yi wa Dokar Ilimi Gyaran Fuska (Education; Minimum Standards Act (Amendment)). An yi wa ƙudurin karatun farko.
  8. 2019: Ƙudurin Kwalejojin Ilimi na Tarayya (Federal Colleges of Education Bill). An yi wa ƙudurin karatun farko.
  9. 2020: Ƙudurin kafa Hukumar Ilimin Malaman Makaranta (National Commission for Teachers Education Bill). An yi wa ƙudurin karatun farko.
  10. 2021: Ƙudurin kafa cibiyar horas da sojoji ilimin kimiyya da nazarin muhalli ta ƙasa (Nigerian Army Institute of Technology and Environmental Studies (Establishment) Bill). An yi wa ƙudurin karatun farko.
  11. 2021: Ƙudurin yi wa dokar Satar Fasahar Kasuwanci gyaran fuska (Trade Malpractices (Miscellaneous Offences) Act (Amendment) Bill). An yi wa ƙudurin karatun farko.
  12. 021: Ƙudurin Kasafin Kuɗi na Musamman (Supplementary Appropriation Bill). An yi wa ƙudurin karatun farko.

Kwamatoci

  1. 1999 - 2003: Shugaban Kwamatin Kasafin Kuɗi a Majalisar Wakilai.
  2. 1999 – 2003: Mamba a Kwamatin Hasken Wuta (Power) a Majalisar Wakilai.
  3. 2001: Mamba a Kwamatin Sabunta Hanyoyin Kasafin Kuɗi na Najeriya a zamanin shugaban ƙasa Obasanjo.
  4. 2009: Mamba a Kwamatin Kyautata Kasuwancin Jihar Kano.
  5. 2015: Farko Mataimakin Shugaba, daga baya kuma Shugaba a Kwamatin Ariziƙin Manfetur a Majalisar Dattawa (Committee on Petroleum Resources (Downstream)).
  6. 2016: Shugaban Kwamatin Manyan Makarantu da Gidauniyar Tallafin Ilimin Manyan Makarantu (TETFund) a Majalisar Dattawa.
  7. 2016: Mamba a Kwamatin Neja-Delta; Kwamatin Masana'antu; Kwamatin Sufurin Ƙasa da sauransu.
  8. 2019 zuwa yau: Shugaban Kwamatin Kasafin Kuɗi a Majalisar Dattawa (Appropriations Committee).
  9. 2019 zuwa yau: Sakataren Ƙungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya.

Sanata Barau I Jibrin Barau Zaune a Tsakiya; tare da Mai Girma Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, OFR daga dama hagu kuma Wakilin Ministan Ayyuka. A Lokacin Ƙaddamar da Aikin Titin Kano Zuwa Dayi
Hoto:Ministry of Information

Gudunmawa

Bisa la’akari da irin muƙaman da ya riƙe da kuma shekarun da ya ɗauka a Tagwayen Majalisun Najeriya da sauran muƙaman da ya riƙe da kuma tarin ƙudurorin da ya gabatar, mai karatu zai gamsu cewa mai kamar zuwa akan aika kuma tabbas da ganin kura za ta ci akuya. Zaman Sanata Barau a waɗancan kujeru da suka gabata ana iya cewa kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Kaɗan daga cikin tarin ayyukan raya ƙasa da Barau ya gabatar akwai:

  1. Tabbatar da ikon zuwa aikin yi wa ƙasa hidima ga ɗaliban buɗaɗɗiyar jami’ar Najeriya (NOUN). A lokacin da yake shugabatantar Kwamatin Manyan Makarantu da Asusun Tallafin Karatun Manyan Makarantu, Sanata Barau ya yi uwa ya yi makarɓiya wajen ganin samuwar wannan doka, abin da daga ƙarshe ya daidaita jami’ar da sauran jami’o’i aka daina yi mata kallon hadarin kaji; labarin da ita jami’ar da kanta ta wallafa a shafinta (NOUN, 2018) domin lamarin ya yi mata daɗi.
  2. 2021: Samar da aikin gina titi mai tsawon kilomita 90.65 da ya tashi daga Kano zuwa Katsina (Construction of Kano-Gwarzo-Dayi Federal Highway).
  3. 2021: Samar da ayyukan gina Rassan Tashoshin Raba Hasken Wutar Lantarki (Electricity Substations) a ƙananan hukumomin Bichi da Ɓagwai.

Lambobin Yabo/Kyaututtukan Girmamawa

  1. 2017: Ya karɓi lambar yabo ta Gwarzon Shekara na Sanatocin Arewa (Northern Senator of the Year 2017), daga Reshen Yaɗa Labarai na Majalisar Dattawa (Senate Press).
  2. 2021: Ya karɓi lambar yabo a Majalisar Dattawa mai taken Jagoran Farfaɗo da Matakan Kasafin Kuɗi (Budget Cycle Restoration Facilitator Award) na shekarar 2020.

Ayyuka

Ayyukan da Sanata Barau I Jibrin ya malala suna da tarin yawa. Daga cikin ire-irensu akwai:

  • Gina Rassan Jami'ar Karatu Daga Gida ta Ƙasa a ƙananan hukumomi 13. Ga samfurin ɗaya daga cikinsu:

  • Hoto:Amaz Zakirai


    Hoto:Amaz Zakirai


    Hoto:Amaz Zakirai


    Hoto:Amaz Zakirai


    Hoto:Amaz Zakirai

  • Raba Motoci 13 ga kowane reshe na jami'ar. Ga samfuri a ƙasa:

  • Hoto:Amaz Zakirai


    Hoto:Amaz Zakirai


    Hoto:Amaz Zakirai

  • Ɗaukar mutane 13 aiki a kowace ƙaramar hukuma da wannan reshen jami'a yake domin aiki a jami'ar
  • Raba Babura Masu Ƙafa Uku Guda 52

  • Hoto:Isiyaku Abubakar Balan


    Hoto:Isiyaku Abubakar Balan

  • Rarraba Kayan Karatu ga Ɗalibai

  • Hoto:Jameel Nohd Ishaq


    Hoto:Jameel Nohd Ishaq

  • Raba Motoci ga Manya-Manyan Limamai

  • Hoto:Bashir Usman Jibaga


    Hoto:Bashir Usman Jibaga


    Hoto:Bashir Usman Jibaga

  • Gina Titin Ɗangaɗa Zuwa Durgu a Ƙaramar Hukumar Ɓagwai

  • Hoto:Jameel Nohd Ishaq


    Hoto:Jameel Nohd Ishaq


    Raba Mashina ga Dagatan Kano ta Arewa
    Hoto:Bashir Usman Jibaga


    Raba Tallafin Taki
    Hoto:Bashir Usman Jibaga


    Gina Ajujuwan Kwamfuta
    Hoto:Bashir Usman Jibaga


    Gina Ajujuwa a Makarantun Firamare
    Hoto:Bashir Usman Jibaga


    Gina Titi
    Hoto:Bashir Usman Jibaga


    Gina Titi daga Kano Zuwa Dayin Jahar Katsina
    Hoto:Bashir Usman Jibaga

Manazarta:

Danmusa I (2021). Senator Barau Lauds FG Over Award of Two Electricity Substation in Bichi, Kabo at N3.3bn. An ciro a shekarar 2021 daga shafin https://www.solacebase.com/2021/03/11/senator-barau-lauds-fg-over-award-of-two-electricity-substation-in-bichi-kabo-at-n3-3bn/

Lamai S. (2021). FG Flags-off N62.7bn Construction of Kano-Gwarzo-Dayi Federal Highway. Federal Ministry of Information and Culture. An ciro a shekarar 2021 daga shafin https://fmic.gov.ng/fg-flags-off-n62-7bn-construction-of-kano-gwarzo-dayi-federal-highway/

News Agency of Nigeria (2021). Senate President Lawan Bags Leadership Award. An ciro a shekarar 2021 daga shafin https://www.pulse.ng/news/politics/senate-president-lawan-bags-leadership-award/73hn17ɓ

NOUN (2019). Historic Passage of Noun Amendments in Senate Sees Graduates Head to NYSC, Law School. An ciro a shekarar 2021 daga shafin https://www.nou.edu.ng/news/historic-passage-noun-amendments-senate-sees-graduates-head-nysc-law-school

Plac Billstrack (2016). Bills Sponsored / Co-sponsored by Sen. Barau Jibril. An ciro a shekarar 2021 daga shafin https://placbillstrack.org/legislatorbills.php?getname=562

Wikipedia (2021). Barau I Jibrin. An ciro a shekarar 2021 daga shafin https://en.wikipedia.org/wiki/Barau_I_Jibrin


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub